Labarai
Shugaban kwalejin fasaha ta Kano ya musanta zargin da ake yi musu
Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Polytechnic Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya musanta zargin da kungiyar malaman kwalejin ta ASUP da kungiyoyin dalibai suka yi na cefanar da wasu filaye mallakin makarantar.
Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya bayyana hakan ne yau, jim kadan bayan wata zanga-zangar lumana da ta wakana da safiyar yau a harabar makarantar, a wani mataki na nuna fushin su kan zargin da suke yi cewar Gwamnatin Kano ta dau gabarar siyar da wani bangare na kwalejin, wanda hakan suka ce kai ya barazana da ci gaban harkar ilmin daliban.
An zargi shugabar makaranta da amsar kudin dalibai
An dage yanke hukunci a shari’ar takardun makarantar Shugaba Buhari
Mahukunta sun rufe makarantar KCC Kano
Wakilin mu Umar Idiris Shu’ibu ya rawaito mana cewa, farfesa Kurawa ya kuma kara da cewa, shakka babu Gwamnatin Kano ko kadan bata dauki wannan mataki ba. A maimakon haka ta maida hankali ne wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwar dalibai.
Shugaban kwalejin ya kuma bada tabbacin gabatar da koken kungiyar ASUP ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, don ganin an kare muradan su da suka shafi ci gaban dalibai.