Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dage tafiyar da zai yi sakamakon rashin tsaro

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗage tafiyar da ya shirya yi a yau zuwa Afirka ta kudu da kuma Angola, a yayin da ya ke jiran sauraron rahoto game da sace ɗalibai da aka yi a Kebbi da harin da aka kai kan wani coci a Kwara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yauwansa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaban ya umurci a aika ƙarin jam’ian tsaro karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara inda lamarin ya faru kamar yadda gwamnan jihar ya buƙata, tare kuma da bai wa ƴansanda umurnin farauto ƴan bindigar da suka kai hari kan masu ibadar.
You must be logged in to post a comment Login