Labarai
Shugabancin kasuwar Singa ya bukaci gwamnati ta tallafa wa mutanen da suka samu gobara

Shugabancin kasuwar Singa ya bukaci gwamnatin jihar Kano, ta tallafawa wadan da iftila’in Gobarar a faru da su a daran jiya, kirin nasu ma zuwa ne a dai dai lokacin da gamayyar shugabancin kasuwar suka gudanar da zagayen jajantawa ga al’ummar kasuwar.
Da ya ke jawabi yayin zagayen duba barnar da wutar ta yi, shugaban kasuwar ta Singa Barista Junaidu Muhammad Zakari, ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa, wajen ganin cewa gwamnatin jihar Kano tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa.
A nasu bangaren, wasu daga cikin yan kasuwar da iftila’in Gobarar ya shafa, sun bayyana cewa wutar da ta tashi ta lakume musu kayayyakin masarufi na miliyoyin Naira, don haka suke bukatar dauki.
You must be logged in to post a comment Login