Labarai
Shugabancin Tinubu na tafiya bisa adalci wajen yin ayyukan raya ƙasa- Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta ce, shugabancin Bola Ahmed Tinubu ya na tafiya bisa adalci wajen rarraba ayyukan raya ƙasa a dukkan yankunan Najeriya.
Ministan yaɗa Labarai Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa manyan ayyuka kamar titin Lagos zuwa Calabar da na Sokoto zuwa Badagry da gadar Second Niger Bridge da kuma layin dogo a Kano sai Kaduna da Lagos, sun tabbatar da cewa babu wani yanki da aka nuna wa wariya.
Rahotanni sun nuna cewa, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi cin gajiyar ayyukan da sama da naira tiriliyan biyar, amma sauran yankuna su ma sun samu muhimman ayyuka.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin ta jaddada cewa, shirin Renewed Hope Agenda zai tabbatar da cewa babu wani yanki da za a bari a baya wajen ci gaban ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login