Labarai
Shugabannin ƙananan hukumomi 3 sun dawo NNPP daga APC
Jam’iyyar APC mai mulki ta sake fuskantar wani koma-baya yayin da wasu shugabannin kananan hukumomi uku suka sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a Kano.
Wadanda suka koma jam’iyyar sun hada da Hon. Ado Tambai Kwa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, mazabar mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Hon. Kwa ya bar APC zuwa NNPP tare da mataimakinsa Hon. Garba Yahaya Labour da sauran kansiloli daga majalisar Ganduje.
Hakazalika, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, shi ma ya yi rashin babban mai biyayya kuma shugaban karamar hukumarsa ta Nassarawa, Hon. Auwalu Lawan Aramposu, zuwa NNPP.
Hon. Mudassiru Aliyu, dan jam’iyyar APC kuma shugaban karamar hukumar Garun-Malam shi ma ya tsallako zuwa jam’iyyar NNPP.
Da yake karɓar masu sauya shekar da dimbin magoya bayansu a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati a ranar Asabar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba da hazakar ƴan jam’iyyar APC na zuwa jam’iyyar NNPP.
Gwamna Yusuf wanda ya ba da tabbacin cewa za a yi adalci da daidaito a sabuwar jam’iyyar tasu, ya jaddada cewa NNPP za ta yi rawar gani wajen karbar daukacin ƴaƴyan jam’iyyar APC domin yi wa al’umma hidima.
Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnati na bunƙasa zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar zuba jari mai yawa a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, albarkatun ruwa domin karfafa rayuwar al’umma.A cewar Gwamna Yusuf,
“Mun yi sa’a da wasu daga cikinku sun fahimci tsarin shugabancinmu, kuma suka yanke shawarar hada hannu da mu domin ciyar da kano gaba.”
Ficewar ƴaƴan jam’iyyar APC zuwa NNPP na zuwa ne makonni biyu kacal, bayan da Shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon Gwamna Ganduje ya mika wata budaddiyar wasika da ya gayyaci shugabannin NNPP zuwa jam’iyya mai mulki.
You must be logged in to post a comment Login