Kiwon Lafiya
Shugabannin kasahen renon Ingila na shirin zaben sabon jagoran kungiyar
Shugabannin Kasashe Renon Ingila na shirin zaben sabon jagoran kungiyar a taron su da zai gudana a cikin wannan makon, kamar yadda fadar Firaministan Birtaniya ta sanar.
Sabon jagoran da ake sa ran sanarwa zai maye gurbin Sarauniya Elizabeth ta Ingila mai shekaru 91 wadda take a matsayin jagorar kasashen tun bayan mutuwar mahaifinta Sarki Geoge na 6 a shekara ta 1952, duk da cewa, ba gadon kujerar ake yi ba.
Kakakin fadar Firaministan Birtaniya ya bayyana cewa, a wajen taron da ke tafe a ranar Alhamis da Juma’a ne za a san wanda zai jagoranci kungiyar kasashen renon Ingila.
Babbar Sakatariyar Kungiyar Patricia Scotland, ta shaida wa manema labarai cewa, taron zai bai wa shugabannin damar magana da juna sosai.
Babu dai wasu bayanai da ke nuna cewa, ko ‘ya’yan ita sarauniyar ne za su hau kujerar jagorancin kungiyar ta Commonwealth.
Sai dai kuma, babban danta, Yarima Charles mai shekaru 69 ya wakilce ta a taron a shekara ta 2013 a Colombo, kafin sarauniyar ta rage yawan zirga-zirga.