Labarai
Shugabannin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun gana a Bamako

Sojoji masu mulki a Mali da Burkina Faso da Nijar sun gana a Bamako, babban birnin Mali kan tunkarar taɓarɓarewar tsaron da ke ƙaruwa da kuma barazanar da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke yi ga faɗin yankin Sahel.
Ana kuma sa ran shugabannin sun tattauna batun yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba kwanan nan a Benin, har ma da tsare-tsaren kafa wani bankin zuba jari na haɗin gwiwa da wata tashar talbijin ta ɗaukacin yankin.
Ƙasashen uku sun janye ne daga ƙungiyar Ecowas ta ƙasashen Afirka ta Yamma, sannan suka katse alaƙa da Faransa kafin su ɗauki matakin ƙarfafa dangantaka da Rasha.
You must be logged in to post a comment Login