Labarai
Shukar Tumatiri a Jihar Katsina ta gamu da illar tsutsar Ibola
Manoman Tumatur a jihar Katsina na alaƙanta tashin farashin tumaturin da tsadar kayan noma da kuma wasu kwari da suka ce na yiwa tumaturin illa wadda hakan yasa farashin tumaturin ya yi tashin gauron zabi.
Malam Mannir Abubakar mai sayar da Tumatur ne a kasuwar ajewa, ‘yace a baya-bayan nan kafin azumi suna sayar da kwandon Tumatur kasa da dubu biyu, amma yanzu ya yi tashin gauron zabi sakamakon wannan matsalar da suka bayyana a baya’.
Sulaiman Yusuf Bindawa na daya daga cikin manoman dake kokawa cewa yayi ‘yanayin zafin da ake fama dashi a yanzu na kara ta’azzara tsadar tumatir din a kasuwa da kuma wata tsutsa da ke kashe tumaturin tun a gona kafin ya girma.
Manoma da dama na fama da karancin masaniya akan kalar irin tumarin da zasu dasa a cikin zafi da kuma sanin maganin feshi da yadda zasu sarrafa shi a gonaki domin samun yabanya mai kyau.
Ko a Jihar Kano dai manoman tumatur din na cigaba da kokawa dangane da illar ga wannan tsutsar take yiwa shukar tumaturin a yanzu, wanda yake kara ta’azzara karancinsa, dama tsadarsa a fadin Jihar.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login