Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta fara sauraron shari’ar da Balaraba Ganduje ta yi karar tsohon mijinta

Published

on

Kotun Majistari mai lamba 69 da ke Kasuwar Sabon Gari a Kano, ta soAn soma shari’ar da ƴar Gwamnan Ganduje ta kai tsohon mijinta kara bisa zarginsa da ya lakaɗa mata dukama sauraron ƙarar da Asiya Balaraba Ganduje, ta kai tsohon mijinta.

Balaraba Ganduje na zargin tsohon mijin na ta Inuwa Uba da shiga waje ba tare da izni ba, tare da cin zarafinta ta hanyar gwada ƙwanji da yi mata rauni.

Bayan da aka karanta masa waɗannan tuhume-tuhume, tsohon mijin ya musanta.

Daga nan lauyansa Barita Hashimu Isah Mai Ulu, ya nemi da a bada belinsa.

Mai shari’a Ishaq Abdu Aboki ya amince da ba da belin bisa sharaɗin kudin ambato naira 50,000 tare da gabatar da nagartattun mutane biyu su ma kowanne da kudin ambato naira 20,000.

Daga bisani, Kotun ta sanya ranar 25 ga watan Mayun da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!