Labarai
Manoman Tumatur na ci gaba da tafka asara sakamakon barnar Tsutsotsi

Manoma da dama ne suka tafka asara sakamakon yadda irin wadannan tsutsotsi ke yin barna tamkar wutar daji zuwa yanzu.
Alhaji Lawan Sulaiman Gurjiya, manomin Tumatur ne a kramar hukumar Bunkure, ya shaida wa Freedom Radio cewa, tsutsar ta yi wa makwabtansa da dama barna.
“Alhamdulillah, ni barnar ta ba ta shafi gona ta ba, amma dai makwabtana da dama sun yi babbar asara, muna karfafa zargin cewa a cikin iri ake hado mana da wadannan tsutsotsi kuma cikin mintina kadan da shigarsu gona suke lalata dukkan Tumatur din da suka samu.”
A nasa bangaren, Dakta Bashir Barau, Malami a kwalejin nazarin aikin gona da sarrafa kayan abinci ta tarayya da ke Hotoro a nan Kano, ya bayyana cewa ya kamata manoma su dauki matakan tantance irin da za su shuka don tabbatar da cewa ba ya dauke da tsutsar tare da yin amfani da iri wanda ke da juriyar kamuwa da tsutsar.
Haka kuma, malamin, ya shawarci manoma da su rika sauya gonakin da suke yin noma a kai a kai domin dadewar gona ana yin shuka iri daya na taimaka wa tsutsotsi wajen ci gaba da addabar gonakin da barna.
A baya-bayannan ne manoman tumatir suka koka da cewa tun a farkon watan Maris din shekarar nan ne suka fara ganin bullar tsutsar mai suna Tuta Absaluta, inda ta yiwa dumbin gonaki mummunar barna ta milyoyin naira.
Alhaji Sani Danladi Yada-Kwari shi ne shugaban kungiyar manoma timatir na jihar Kano, kuma sakataren kungiyar na kasa, ya shaida wa manema labarai cewa, tsutsar ta yi mummunar barna a gonaki da dama musamman a jihohin Kano da Jigawa da kuma Bauchi.
You must be logged in to post a comment Login