Labarai
Siyasar Kano: Mahangar masana kan zaben kananan hukumomi
Masana sun fara sharhi kan shirin hukumar zaɓe ta jihar Kano na gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a watan Janairun baɗi.
Dr. Sa’id Ahmad Dukawa na jami’ar Bayero ya shaida wa wakilinmu Bashir Sharfadi cewa, shirin zaɓen a kan lokaci abu ne da ya dace domin zai kawar da tsarin naɗa kantomomi.
Sai dai, ya ce akwai wasu abubuwa uku game da zaɓen da suka kunshi shiri kafin zabe da yayin zaben da kuma bayan zaben.
Dr. Dukawa yace yin adalci a yayin yakin neman zabe da kuma tabbatar da cewa an samarwa da hukumar zabe kayayyakin da take bukata, sai kuma yin adalci a yayin sanar da jam’iyyar da ta lashe zabe, shine abinda ke inganta kowanne irin zabe.
Hukumar zaɓen Kano dai ta yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin tayi karɓaɓɓen zaɓe bisa adalci.
You must be logged in to post a comment Login