Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojin Nijeriya ta gargadi Sojin kasar kan takun sakar Nijar da ECOWAS

Published

on

Rundunar Sojin Najeriya ta yi wa dakarunta kashedi dangane da takun sakar da ke tsakanin gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ta ECOWAS.

Babban hafsan dakarun sojin kasarnan Lt. Janar Taoreed Lagbaja ne yayi wannan gargadi a yayin wata ziyara daya kaiwa dakarun runduna ta 8 dake jihar Sakkwato wadda jihar ke daya daga jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, inda ya bukaci koda yaushe su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, saidai su guji afkawa ba tare da umarni ba

Wannan gargadi dai ya biyo bayan labaran kanzon kurege wasu ke yadawa barkatai a shafukan Sada zumunta na yanar gizo, game da batun.

Takun-saka da ke wanzuwa tsakanin Jagororin Gwamnatin Soji da ta yi juyin mulki a Jamhuriyar da kungiyar ta ECOWAS, na ci gaba da sanya fargaba da rashin tabbas tsakanin al’ummun kasashen biyu musamman a jihohin da kasashen ke makwabtaka da juna.

 

Rahoton: Mukhtar Abdulkadir Birnin Kudu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!