Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ziyarar wasu gwamnonin Arewa zuwa ga Nuhu Ribado ziyara

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare da takwaransa na jihar Niger Muhammad Umar Bago sun ziyarci mai taimakawa shugaban kasa a fannin Mal Nuhu Ribado a ofishinsa a yammacin jiya Alhamis, domin tattaunawa game da matsalar tsaro dake cigaba da addabar jihohin su.

Mai magana da yawun gwamnan Zamfara Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace ‘ziyarar ta zama wajibi a kokarin gwamnonin na lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a jihohin da taki ci taki cinyewa’.

A cewar sanarwar ‘maido da zaman lafiya jihar Zamfara ne babban aikin da gwamnatin Dauda Lawal Dare ta fi sanyawa a sahun gaba tun bayan saba layar kama aiki’.

A yayin ganawar gwamnonin biyu sun tattauna muhimman batutuwa game da sha’anin tsaro da Malam Nuhu Ribadon.

 

Rahoton: Mukhtar Abdulkadir Birnin Kudu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!