Labarai
Sojoji 9 sun mutu sakamakon taka Bam a Borno

Rahotannin da jami’an tsaron Najeriya suka fitar, sun bayyana cewa, aƙalla sojoji tara ne suka mutu lokacin da jerin gwanon motocinsu suka taka wani Bam a jihar Borno.
Wasu sojojin da dama kuma sun jikkata a harin da ya afku a ranar Lahadi.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
BBC ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin da masu iƙirarin jihadi na ISWAP ke gudanar da ayyukansu da kuma kai munanan hare-hare.
You must be logged in to post a comment Login