Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji na bincike kan zargin cin zarafin ɗalibar Sakandire

Published

on

Rundunar sojin ruwan ƙasar nan ta shiga bincike kan zargin cin zarafin wata ɗaliba a makarantar sakandaren sojin ruwa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Mai magana da yawun rundunar Commodore Sulaiman Dahun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa Freedom Radio.

Dahun ya ce, sun samu wani faifan bidiyo daga iyayen wata ɗaliba da malamar makarantar ta yiwa dukan tsiya, har ta yi mata ruɗu-ruɗu da jiki.

Ya ce, kawo yanzu bincikensu ya gano cewa al’amarin ya faru ne tun a zangon karatu biyu da suka wuce.

Ya ci gaba da cewa, rundunar ba za ta lamunci cin zarafin kowane ɗalibi ba, a saboda haka za a tabbatar an ɗauki matakin da ya dace.

A ƙarshe ya yi kira ga iyayen ɗalibai da su kwantar da hankulansu, tare da alwashin hakan ba zai sake faruwa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!