Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Borno

Published

on

Majalisar dattijai ta yabawa rundunar sojin kasar nan sakamakon bajintar da sojoji su ka yi wajen dakile yunkurin kaiwan wani hari da ‘yan boko haram su ka yi a garin Askira da ke jihar Borno.

 

Da ya ke jawabi ga manema labarai jiya a Abuja, shugaban kwamitin kula da rundunar sojin kasar nan na majalisar dattijai, sanata Ali Ndume ya ce labarin da ya samu ya tabbatar da cewa, sojojin sun kashe ‘yan boko haram da dama a garin na Askira.

 

Sanata Ali Ndume ya ce tun farko ‘yan ta’addar wadanda suka taho cikin motoci guda goma sha daya sun yi yunkurin kaiwan harin ne a garin Askira da misalin karfe hudu na yamma, sai dai sun hadu da tirjiya daga sojoji wadanda suka yi musu barna mai yawa.

 

Sanatan ya kuma ce matukar sojoji za su ci gaba da zage dantse bako shakka nan gaba kadan ba da dadewa ba ayyukan boko haram zai zamo tarihi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!