Labarai
Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 12 a Borno

Dakarun Sojojin Najeriya, sun yin nasarar kashe wasu yan kungiyar Boko Haram su 12 a wani samame da suka kai yankuna da dama na jihar Borno.
Gidan talabijin na NTA, ya ruwaito cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka hallaka yan bindigar a ƙaramar hukumar Mafa mai nisan kilomita 59 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ya kara da cewa, dakarun sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri inda suka auka wa sansanonin yan ta’addan a Tamsu da Ngamdu da Dalakaleri da kuma Gaza.
Rahotonni sun bayyana cewa, cikin makamai da kayayyakin da dakarun suka ƙwato daga hannun yan Boko Haram sin har da bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas, da ƙunshin harsasai takwas da kuma miyagun ƙwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login