Labarai
Sojoji sun kama jagoran yan bindiga da ake zargi da addabar matafiya a hanyar Benue zuwa Taraba

Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da cewa, dakarunta sun kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga da ake zargin ya daɗe ya na addabar matafiya a kan hanyar Benue zuwa Taraba.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana a Jalingo cewa wanda aka kama Fidelis Gayama na cikin jerin mutanen da hukumomin tsaro ke nema a jihohin Benue da Taraba.
Ya kuma bayyana cewa, an samu nasarar kama shi ne a ƙauyen Vaase da ke ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa Gayama na da alaƙa ta kusa da wani fitaccen shugaban ƙungiyar ’yan ta’adda da ake nema, Aka Dogo.
Laftanar Umar Muhammad ya ƙara da cewa ana zargin Fidelis Gayama ne jagoran wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke kai hare-hare kan matafiya da al’ummomi a kan hanyar Kente–Wukari da kuma yankunan iyakar Benue da Taraba.
A cewarsa, wanda aka kama yana hannun sojoji a halin yanzu, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login