Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun kara hallaka ‘yan bindiga a Zamfara

Published

on

Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce, dakarun Operation Sanity na Rundunar sojin kasar nan sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga guda shida a jihar Zamfara.

Mukaddashin daraktan yada labarai na shalkwatar tsaro ta kasa burgediya janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce, sojojin wadanda suka samu rakiyar jiragen shalkwabta sun kashe sojojin ne a tsaunin Kolmani da ke kauyen Rukuduwa a yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Ya kara da cewa, tun farko sojojin sun samu labarin cewa ‘yan bindigar suna shirin kaiwan hari ne a kauyen Kasele da ke yankin karamar hukumar Batsari lamarin da yasa ba tare da bata lokaci ba, su ka kai musu hari.

Haka zalika a cewar mukaddashin mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasar, sojojin sun kuma kama wnai mutum mai suna Lawali Maikudi Modu wanda ake zargin shine yake kai wa ‘yan bindigar bayanan sirri kan ayyukan sojoji da kuma wuraren da zasu kai hari.

A cewar burgediya janar Bernard Onyeuko an kama mutumin ne a Marabar Dan Ali da ke yankin karamar hukumar Gusau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!