Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe kwamandan ‘yan ta’addan ISWAP

Published

on

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Haɗin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabshin Najeriya, sun sanar da nasarar kai wasu munanan hare-hare kan ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke addabar yankin.

 

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce bayanan sirri sun tabbatar da kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP mai suna Julaibib a yankin Gujba.

 

A cewarsa, an yi nasarar kashe shugaban mayaƙan na ISWAP ne bayan wani artabu da aka yi tsakanin mayaƙan da dakarun soji a kusa da garin Kimba da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, a ranar 30 ga watan Janairu.

 

“Wannan ci gaba mai mahimmanci ya kasance babban illa ga tsarin ƙungiyar ISWAP a yankin,” in ji sanarwar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!