Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAPS ta samu nasarar kashe kwamandojin ISWAP 3

Published

on

Wata majiya ta shaida wa Zagazola Makama, kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi cewa, kwamandojin ISWAP da suka bakuncin lahira sanadiyyar harin sun hada da Abou Maimuna da Abou Zahra da kuma Kwamanda Saleh.

Bayanai sun ce tun a ranar 10 ga watan Janairun da muke ciki ne rundunar sojin ta kaddamar da wadannan hare-hare masu tasiri karkashin jagorancin Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Air Commodore UU Idris.

Aminiya ta ruwaito cewa, an samu nasara kan mayakan ne yayin da wani jirgin leken asiri na rundunar sojin ya hango ‘yan ta’addan na tafiya a cikin kwale-kwale.

Majiyar Zagazola Makama ta ce mayakan sun yi yunkurin tserewa amma ba su yi nasara ba sakamakon luguden wuta da aka yi musu babu kakkautawa, lamarin da ya yi ajalin kwamadojin uku da mayakansu da dama.

Kazalika, rundunar sojin ta kai wasu hare-hare a kusa a yankunan Ali Sheritti da Kwatan Shallan da ke kusa da garin Kukawa, inda aka kashe wasu ’yan ta’addan na ISWAP da ba a tabbatar da adadinsu ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!