Connect with us

Labarai

Hisba ta kai sumame wasu wurare

Published

on

Hukumar Hisbah tayi nasarar kama wasu matasa da yammata a yayin da suke tsaka da aikata baɗala a wani wurin shakatawa da ke titin Katsina a jihar Kano.

Babban dataktan hukumar Hisbah Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya ne ya sanar da hakan a shalkwatan hukumar da ke unguwar sharada jim kaɗan bayan karɓar rahoto.

Hukumar ta kuma koka kan yadda ake daɗa samun masu aikata miyagun dabi’u musamman ma matasa da suka haɗar da samari da ƴan mata.

Dr. Aliyu Musa ya ƙara da cewa za su ci gaba da zuba idanu domin ganin an lalubo guraren baɗala a jihar Kano da nufin daƙile ayyukan fasadi.

A cewar sa, waɗanda aka kama za a faɗaɗa bincike a kan su tare da ɗaukan matakin da ya dace.

Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Lawan Ibrahim ya aikewa Freedom radio.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!