Labarai
Sojoji sun kashe yan Boko Haram guda 9 a Borno

Dakarun undunar sojin Najeriya ta ce, ta yi nasarar kashe yan ta’addar Boko Haram su tara a jihar Borno.
Dakarun rundunar musamman ta “Operation Hadin Kai” ne suka kashe ‘yan bindigar a yankunan kananan hukumomin Konduga da Bama da kuma Gwoza.
Rahotonni sun bayyana cewa, yan ta’addar sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ta haɗa Marte da Dikwa kafin sojojin su fatattake su, tare suka gano bama-bamai guda 17 a ƙarƙashin gadar.
Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, dakarun rundunar sun yi wa yan Boko Haram din kwanton Bauna ne bayan yi masu ƙawanya, yayin da a gefe guda kuma jiragen sama ke yi musu luguden wuta, lamarin da ya sa aka kashe tara daga cikinsu.
Daga cikin tarin makaman da aka ƙwace daga hannun yan ta’addar sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 da kirar PKT a ƙananan hukumomin Konduga da Bama da kuma Gwoza.
You must be logged in to post a comment Login