Labarai
Sojoji sun kubutar da fasinjoji sama da 20 da aka yi yunkurin garkuwa da su

Rundunar Sojojin kasar nan sun dakile yunƙurin garkuwa da wasu fasinjoji a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu a Jihar Benue, inda suka ceto fasinjojin su 24 daga motocin haya biyu da ke tafiya daga Jos zuwa Ibadan.
Ta cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ruwaito bayan samun kiran gaggawa, sojoji sun kai ɗauki bayan da suka yi musayar wuta da ’yan bindigar da suka tsere zuwa daji.
Kwamandan rundunar, Major General Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa gaggawar martani, tare da tabbatar da ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi al’ummar yankin.
You must be logged in to post a comment Login