Labarai
Sojojin Congo da mayaƙan da ke taimaka musu sun fara komawa sassan birnin Uvira

Sojojin Jamhuriyyar Congo da mayaƙan da ke taimaka musu a yaƙin da ƴan tawaye sun fara komawa sassan birnin Uvira na gabashin ƙasar kwanaki bayan janyewar mayaƙan M23 masu samun goyon bayan Rwanda.
Mayaƙan M23 sun ƙwace iko da babban sansanin sojojin Congo da ke birnin Uvira mai iyaka da ƙasar Burundi a ranar 10 ga watan Disamban shekarar data gabata, bayan ganawar shugaba Trump da shugabannin kasashen na Congo Felix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame a fadar Washington da ya kai ga ƙulla yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.
Kama ikon da sansanin ya janyo ma ‘yan ta’addan gagarumin nasara cikin watanni 10 wanda ya haddasa matsanancin firgice da tsoro a zukatan mazauna yankin tare sanadin ɓarkewar rikici da mutuwar dubban mutane da raba dubbai da muhallan su.
You must be logged in to post a comment Login