Labarai
Sokoto: Mutane 7 sun rasu sakamakon fashewar Bam

Akalla mutane bakwai ne suka rasu bayan wani Bam, ya tarwatse a ƙauyen Gwabro da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.
Lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya Litinin, a lokacin da waɗanda abin ya rutsa da su ke dawowa daga yawon Sallah a kan babura.
Rahotanni sun nuna cewa an dasa bama-baman ne a ƙarƙashin wata itaciya da sojoji ke amfani da ita a matsayin wajen hutu yayin sintiri.
Bayan fashewar, mutum shida sun mutu nan take, yayin da ɗaya daga cikin yara biyu da suka jikkata ta rasu washegari.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Alhaji Ghazzali Rakah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa waɗanda suka mutu mazauna ƙauyen Zurmuku ne, wanda ke maƙwabtaka da inda lamarin ya faru.
You must be logged in to post a comment Login