Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale

Published

on

Akalla ƴan mata goma sha biyar ne suka rasu bayan kifewar kwale-kwale a ƙauyen Dandeji da ke karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce ƴan matan na kan hanyarsu ta zuwa wani daji da ke kusa domin neman ita ce, lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a safiyar ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ƴan mata sama da 40 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da lamarin ya faru, a cewar shaidu.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim, an gano gawawwaki goma sha biyar zuwa lokacin fitar da rahoton.

Ya ce, masu ninƙaya za su ci gaba da neman sauran waɗanda lamarin ya ritsa da su.

A nasa bangaren, Shugaban karamar hukumar ta Shagari, Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda kuma ya kara da cewa, tini aka yi wa wadanda suka rasu jana’iza.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!