Kasuwanci
SON: Mun kone maganin sauro da jabun wayar wutar lantarki na naira miliyan 8 a Kano
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa (SON), ta kone wasu tarin maganin sauro da wa’adin amfanin su ya kare tare da wayar wuta marsa inganci na fiye da naira miliyan takwas a nan Kano.
Hukumar ta kone kayan ne da tsakar ranar yau Laraba a garin Yanka Tsari da ke yankin karamar hukumar Dawakin Kudu.
Da ya ke shaida lalata kayan marasa kyau, jami’in da ke kula da shiyyar arewa maso yamma na hukumar Alhaji Muhammad Usman Sheshe wanda ya wakilci shugaban hukumar ta SON na kasa Malam Farouk A. Salim, ya ce, kayan sun hadar da nadi 380 na wayar wuta maras kyau tare da jaka 4,600 na maganin sauro da wa’adin amfani da su ya kare.
A nasa bangaren, shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano Alhaji Yunusa Muhammad Baina, ya ce, hukumar ta kame kayan ne a wani rumbun adana kaya da ke birnin Kano bayan da ta samu bayanan sirri akan boye su.
Haka zalika hukumar kula da kare hakkin masu sayen kaya ta kasa (FCCPC) shiyyar Kano da hukumar kare muhalli ta Najeriya (NESREA) da jami’an hukumar Civil Defence na daga cikin hukumomin gwamnati da suka halarci bikin banka wa kayakin wuta.
You must be logged in to post a comment Login