Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An nada sabon Sarkin Kagara

Published

on

Gwamnatin jihar Naija ta nada dagacin yankin Yakila Ahmad Garba Gunna a matsayin sabon sarkin Kagara.

Ahmad Garba Gunna mai shekarau 46 shi ne mukaddashin shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Naija kuma shi ne Dan Majen Kagara ya samu nasarar ne bayan da ‘yan majalisa masu zabar sarki 14 suka tantance shi cikin sunayen mutane biyar da aka zaba.

Wannan dai na cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Naija Abubakar Sani-Bello ya fitar, ta hannun kwamishinan kananan hukumomi, da ci gaban Al’umma da kuma harkokin aasarautu, Malam Abdulmalik Sarkin Daji a yau Laraba.

Cikin sanarwar gwamnan ya ce nadin sabon Sarkin ya biyo bayan amfani da sashi na 3 karamin sashe na 1 cikin baka, na Dokar Sarakuna da kuma Fasali na 19 na dokar jihar Neja.

Idan za a iya tunawa tsohon Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko Kagara ya rasu a ranar 1 ga Maris na shekarar 2021 bayan ya sha fama da rashin lafiya a Minna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!