Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Son rai da son zuciya ne ya hana ƙasar nan ci gaba – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa anan kano ya ce, son rai da son zuciya ne ya hana ƙasar nan ci gaba.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ne ya bayyana haka a zantawarsa da Freedom Radio.

Farfesa Fagge ya ce ” Akwai matsaloli da dama wajan gudanar da sha’anin mulki a ƙasar nan, dalilin kenan da ya hana mu ci gaba”.

“In dai har ana son a samu haɗin kai da ci gaban siyasa a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya to dole sai an cire son rai da son zuciya” a cewar Fagge.

Farfesa Kamilu Fagge ya ƙara da cewa ƙasashen da ake kallon sun ci gaba ba yanayin irin siyasar ƙasar nan suke yi ba.

“Kasashen na gudanar da mulki ne ba son zuciya ba son rai shiyasa suke samun ci gaba, kuma da za mu yi koyi da su, za mun fita daga halin da muke ciki” in ji Farfesa Fagge.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!