Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tsaro

Soyayya ta sa wani matashi ya sha guba ya mutu a Katsina

Published

on

Rahotannin da Freedom Radio ta samu daga garin Kafur na jihar Katsina sun ce wani matashi ya sha guba har yace ga garinku saboda soyayya tsakaninsa da masoyiyarsa.

Bayanai sun ce matashin mai suna Abdullahi ya sha gubar ne ba don sun samu sabani da budurwarsa ba, sai dai don iyayensa sun ce ya tsagaita a aurar da kannensa mata biyu sannan a yi nasa auren.

Wata majiya daga garin na Kafur da wakilinmu daga Katsina ya zanta da ita ta wayar salula ta ce wannan shawarar ce matashin mai kimanin shekaru 20 ya ga kamar za a yi tashin duniya kafin lokacinsa ya zo, ya yanke shawarar yanke wannan hukunci da wasu ke ganin danyen-hukunci ne.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, tace an tashi da matashin da safiyar Asabar din nan lafiya lau, amma ya nemo maganin kwari, ya hada da fetur ya sha, ba da jimawa ba yace ga garinku nan.

Tuni dai an yi jana’izar sa a cikin garin na Kafur a daidai lokacin da bayanai ke cewa iyayensa da na budurwar da zai aura din da ita kanta budurwar duk sun shiga rudani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!