Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Sule Lamido ya zargi gwamnatin APC da gaza cika alƙawuran da tayi

Published

on

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamiɗo, ya ce fifita buƙatun kai da wasu shugabannin siyasa ke yi a arewacin ƙasar nan, shi ke haddasa matsalolin tsaron da ke ƙara ta’azzara.

Sule Lamiɗo ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar sa shekaru 73 a duniya. Ya kuma zargi Gwamnatin APC da gaza cika alƙawuran da ta yi, baya ga ɗora mutane kan aikata abu bisa doron son zuciya.

Tsohon Gwamnan ya ƙara da cewa, matukar ana son kawo karshen matsalolin da Najeriya ta shiga, to dole sai shugabanni da malamai a kowane bangare sun ajiye son rai, tare da haɗa kai a matsayin ƙasa guda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!