Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sulhun Kwankwaso da Ganduje Alkhairi ne – Ƙalarawi

Published

on

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Kano Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya ce, yin sulhu tsakanin shugabannin manyan jam’iyyun siyasar ƙasar nan alkhairi ne ga alummar Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba.

Yana mai cewa, kwankwaso da Ganduje sun daɗe tare kafin su samu rabuwar kawuna a tsakanin su.

Ƙalarawi ya yi zargin cewa “Shaiɗan da shaiɗanun mutane ne suka shiga tsakanin shugabannin biyu, kuma suka yi nasarar ƙulla gaba mai ƙarfi”.

Ya kuma buƙaci malaman Kano da su yi kikari wajen sulhunta su maimakon a ce wasu ne za su yi hakan.

Sheikh Tijjani Bala, ya kuma yi kira ga gwabnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya yi amfani da matakin da ya ɗauka na kafa kwamitin shawarwarin da ya ke shirin samarwa domin ci gaban Jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!