Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ta’addanci: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 tare da kashe mutum 1 a jihar Niger

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka bakwai da ke cikin garin Gurmana a karamar hukumar Shiroro a jijar Naija, tare da kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da wasu 10.

Kauyukan da abin ya shafa su ne: Karibo, Shekadna, Kokki, Sarkin Zama, Bakin Kogi, Maganda da sauran Kauyukan da ke kusa da su duk a karkashin Gundumar Gurmana.

Hakimin Sarkin Zama da wasu da dama da suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga a halin yanzu suna kwance a asibitoci daban-daban da ke Kuta shedkwatar karamar hukumar Shiroro.

Rahotannin sun bayyana cewa yan fashin sun zagaya cikin garuruwan akan Babura suna kona gidaje da rumbunan jama’a tare da yin harbi kan mai uwa da wabi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!