Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Yanzu-yanzu-Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aiki

Published

on

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aikin da ta tsunduma a duk fading kasar nan.

Wannan na zuwa ne kwanaki 10 bayan da likitocin suka fara yajin aikin, lamarin da ya jefa marasa lafiya da dama cikin halin rashin kulawa.

Shugaban kungiyar, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi ne ya tabbatar da dakatar da yajin aikin ga gidan talabijin na Channels a Asabar din nan.

Dakta Okhuaihesuyi ya ce shugabannin kungiyar sun dauki matakin dakatar da yajin aikin ne biyo bayan ganawar da suka yi da mambobin wanda suka dauki kimanin awanni 15 suna yi.

Ya ce, kungiyar za ta kara yin jawabi a taron manema labarai kan shawarar da ta yanke a Lahadi mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne awanni kadan bayan ganawa tsakanin shugabannin kungiyar kwadagon da gwamnatin tarayya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!