Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ta’ammali da miyagun kwayoyo na kassara garkuwar jiki – Masana Lafiya

Published

on

Masana kiwon lafiya sun ce shan miyagun kwayoyi na yin mummunar illa ga lafiyar mutane musamman ma kwakwalwa, da wani sa’in ma ke kaiwa ga asarar rai.

Wakiliyarmu Halima Wada Sinkin ta yi nazari kan yadda wasu mata musamman ma ma’aurata ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, lamarin da ya sanya ta hada wannan rahoton.

Salon shaye-sayen miyagun kwayoyin ya kasu daban-daban, inda wasu ke sha ta hanyar amfani da shisha, inda ma aka samu karin wuraren shan shisha a nan Kano da dama.

Inda wasu suke zuba kwayoyin a cikin shishar da suke zuka, ba tare da jin tsoro ko kunya ba.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce illar da shisha ke yi wa lafiya ta ninka ta taba sigari.

Wani kwararren likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano Dr Aminu Shehu ya shaidawa Freedom Radio irin illolin da shan miyagun kwayoyin ke yi wa bil’adama.

Isah Likita Muhammad shi ne sabon shugaban hukumar yaki da sha fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Jihar Kano, ya ce suna nan suna bincike a kan masu aikata wannan dabi’a don daukar matakin da ya dace a kai.

Isah Likita ya ce, “Duk wanda muka kama yana sha ko sayar da miyagun kwayoyi zai mu dauki matakin da ya dace a kansa, kuma ba za mu saurara wa duk wani ma’aikacin hukumar da aka samu da hannu cikin wannan mummunar dabi’a ba.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!