Labarai
Tabbatar da Ramat a matsayin shugaban NERC zai magance matsalar lantarki- Masu Kamfanoni

Gamayyar kungiyoyin yan kasuwa da masu kananan da matsakaitan masana’antu da ke nan Kano, sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma majalisar dattawa da su tabbatar da Injinya Ramat Garba Abdullahi, a matsayin sa na shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeiya NERC.
Mai magana da yawun kungiyoyin yan kasuwar Muhammad Sadik, ne ya bukaci hakan yayin taron manema labarai da kungiyoyin suka gudanar da yammacin Litinin din makon nan.
Kungiyoyin sun bayyana cewa, suna da kwarin gwiwar tabbatar da Injinya Ramat Garba Abdullahi, a matsayinsa na shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa, zai taimaka wajen magance matsalolin wutar lantarki da ake fama da ita a fada fadin kasar nan.
Haka kuma, sun yaba wa shugaba Tinubu bisa zabo Injinya Ramat Garba Abdullahi, domin nada shi a wannan matsayi da cewa, shugaba Tinubu ya yi haka ne bisa cancanta da kwazo.
kungiyoyin sun kuma bukaci majalisar Dattawa da ta tabbatar da Injinya Ramat Garba Abdullahi, ba tare da bata lokaci ba.
Wannnan dai na zuwa ne yayin da ake ta samun cece-kuce kan shirin tantance Injinya Ramat Garba Abdullahi, bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabe shi a matsayin matsayin sa na shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeiya NERC.
You must be logged in to post a comment Login