Connect with us

Labarai

Tallafawa Matasa : Buhari ya ce wasu jihohi za su sami mafi tsoka

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce jihohin Kano da Lagos da Kuma Abia, za su samu kaso mafi tsoka a shirin da ta fito da shi na tallafawa matasan kasar nan don farfado da tattalin arzikikin su mai taken Survival Fund.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Laolu Akande ne ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya lahadi.

Ya ce jihohin Kano da Lagos da Abia suna gudanar da harkokin kasuwanci fiye da sauran jihohin kasar nan, saboda haka aka zabe su a matsayin jihohin da zasu fi amfana da shirin.

Sai dai y ace hakan b wai yana nufin sauran jihohin kasar nan da birnin tarayya ba zasu amfana da shirin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,845 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!