Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Tammy Abraham zai bugawa kasar Ingila wasa sabanin Nijeriya

Published

on

Biyo bayan kin bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila Tammy Abraham cikin jerin sunayen da zasu wakilci Nigeria, mai haras da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa kasar Ingila Gareth Southgate ya sanya sunan dan wasan cikin ‘yan wasan da zasu wakilci kasar ta Ingila a wasannin da zata fafata a kwanannan.

Tammy Abraham dai yana da damar ya zabi kasar kasar da zai bugawa wasa tsakanin Nijeriya da Ingila, sai da mai horas da ‘yan wasan Nigeria Gernot Rohr yace a yanzu haka Nijeriya  bata bukatar dan wasan.

Dan wasan mai shekaru 22 yanzu haka ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kwallaye 7 a wasanni 7 da ya buga a gasar Primiyar kasar Ingila a kakar wasanni ta bana.

Nijeriya dai tana fama da matsalar ‘yan wasan gaba biyo bayan ritaya da Odion Ighalo ya yi.

Sai dai har yanzu Gernot Rohr bai gama gamsuwa da yadda Abraham ke taka leda ba, a don haka yake ganin yanzu Nijeriya tana da manyan ‘yan wasa wadanda suka fi Tammy Abraham iya wasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!