Labarai
Taraba:An sanya dokar takaita zirga-zirga a garen Jalingo sakamakon rikicin kabilanci
Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, ya sanya dokar takaita zirga-zirga a garin Jalingo babban birnin jihar biyo bayan wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Kona da ATC da ke kusa da Jalingo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Bala Dan Abu.
Sanarwar ta ce, sakamakon sabon rikici da ya barke a garin Kona da ATC da ke daf da garin Jalingio, gwamnatin jihar Taraba ta ga dacewar sanya dokar tabaci a Jalingo da kuma garuruwa biyu da lamarin ya faru.
A cewar sanarwar, dokar takaita zirga-zirgar, za ta ci gaba da gudana ne har illa-masha-Alla, kuma daga karfe hudu na yamma zuwa shida na safe.
Gwamna Darius Ishaku ta cikin sanarwar dai, ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbata duk wani mazaunin jihar, ya yi biyayya ga dokar takaita zirga-zirgar, har zuwa lokacin da lamura zasu kyautata.