Labarai
Taron ECOWAS : Buhari zai gana da takwarorin sa a Jamhuriyyar Nijar
Shugabannin ƙungiyar cigaban tattalin arzikin yammacin ƙasashen Afirika ECOWAS za su gana a Jamhuriyyar Nijar a yau Litinin don tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi yankin.
Taron na kwana ɗaya, kuma shi ne irin sa na 57 kuma zai gudana ne a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ranar Litinin.
Rahotanni sun ce taron zai tattauna kan yanayin da ake ciki a Mali, da suk haɗa da sake duba takunkuman da aka ƙaƙaba bayan juyin mulkin da aka yi ranar 18 ga Agusta.
Shugabannin ƙasashen Najeriya da suka hadar da Senegal da Cote d’Ivoire Burkina Faso Najeriya na daga cikin mahalarta taron.
Sai dai baya ga batun Mali, a wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar ranar Lahadi ta bayyana cewa taron zai mayar da hankali ne kan tattalin arziki da annobar korona da kuma tsaro.
You must be logged in to post a comment Login