Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ceto ‘yan Najeriya da aka yi safarar su zuwa kasar Labanon – Minista

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sake ceto rukunin ‘yan kasar nan da aka yi safarar su zuwa kasar Labanon su ashirin da bakwai a jiya Lahadi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyema ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun ministan Ferdinand Nwonye.

Ya ce dawo da ‘yan kasar nan daya ne daga cikin alkawuran da gwamnatin tarayya ta yi na tabbatar da babu wani dan kasar nan da ke kasar ta Labanon da sunan bauta.

Geoffrey Onyema ya kara da cewa, da dama yan kasar nan da suka amince aka tafi da su kasar Labanon kuma suke cikin tsaka mai wuya tare da neman agaji, a don haka gwamnatin tarayya ba za ta amince da ganin yan kasar nan na shan wahala ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!