Labarai
Tattalin arzikin Najeriya ya samu tagomashi a zangon farko na 2021 – NBS
Wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar a jiya Lahadi ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu tagomashin kasa da digo daya a zangon farko na wannan shekarar duk kuwa da fama da ake da cutar corona.
Wannan rahoton ya nuna cewa akwai alamun ci gaba idan aka kwatanta da koma bayan da tattalin arzikin na kasar nan ya shiga a zango na biyu da na uku a shekarar da ta gabata.
Sai dai duk da haka bunkasar tattalin arzikin bai kai na zangon farko na shekarar da ta gabata ba wanda ya kai kaso daya da digo tamanin da bakwai.
Hukumar ta NBS ta ce wannan ya nuna alamar farfadowa da tattalin arzikin na Najeriya ya yi, sakamakon mashash-sharan da ya fada sanadiyar cutar covid-19
You must be logged in to post a comment Login