Barka Da Hantsi
Tattaunawa kan matsalolin yaye ɗalibai da tsarin samun gurbin karatu a makarantun kiwon lafiya na Kano
A cikin shirin na wannan ranar, an yi duba ne kan matsalolin yaye ɗaliban kiwon lafiya da tsarin samun gurbin karatu a makarantun kiwon lafiya na Kano da kuma yadda wasu ɗaliban ke faɗawa hannun ƴan damfara da suke buɗe asusun banki da sunan makarantu a lokutan daukar sabbin dalibai.
Baƙin da aka tattauna dasu sun haɗa da Comrade Bello Ɗalhatu shugaban makarantar kiwon lafiya ta School of health technology Kano da kuma Hajia Manubia Abdu Jibril shugabar makarantar koyon aikin unguwan zoma ta school of midwifery Kano.
You must be logged in to post a comment Login