Labarai
Tawagar gwamnatin tarayya ta yi ta’aziyyar Alhaji Bashir Usman Tofa
Tawagar gwamnatin tarayya ta kai wa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ziyarar ta’aziyyar rasuwar Alhaji Bashir Usman Tofa.
Tawagar na ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro Manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya a jiya Litinin.
Da yake karbar ta’aziyyar sarkin yace, ba iya Kano kaɗai rashin ya shafa ba, domin kuwa Alhaji Bashir Tofa yaba da gudunmuwa wajen tafiyar da ci gaban ƙasar nan.
“Lallai mun sani rashin Alhaji Bashir Usman Tofa rashi ne babba, da ya shafi ɓangarori da dama sai dai muna fatan Allah ya jiƙansa da gafara”.
A nasa jawabin ministan tsaro Manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya mika ta’aziya ga iyalan marigayin da kuma al’ummar jihar Kano a madadin gwamnatin tarayya.
“Mun zo don mu jajantawa al’ummar Kano da masarauta da iyalan Marigayi Alhaji Bashir Usman Tofa, domin mun sani irin wannan mutuwar babban rashi ne a ƙasa, kuma muna addu’ar Allah ya sa can tafi nan”.
A cikin tawagar ta ƙunshi ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamj da akanta janar na ƙasa Ahmed Idris sai kuma mai magana da ya yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu.
You must be logged in to post a comment Login