Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Tennis: Ashleigh Barty za ta fafata wasan ƙarshe da Danielle Collins

Published

on

‘Yar wasan kasar Australia Ashleigh Barty ta zama ta farko data kai ga wasan karshe na gasar Australian Open bayan shekaru 42 bayanda ta samu galaba kan ‘yar wasa Madison Keys a karawar da suka yi a wasan kusa da karshe a ranar Alhamis a filin wasa na Rod Laver Arena.

Barty mai shekaru 25 ta samu nasara kan Keys ‘yar kasar Amurka mai shekaru 26 da ci 6-1 da 6-3.

‘Yar wasa Barty za ta fafata wasan karshen da ‘yar wasan kasar Amurka, Danielle Collins a ranar Asabar.

‘Yar wasa Collins mai shekaru 28 ta samu nasarar kaiwa ga wasan karshe a gasar ta Australian Open ne bayanda ta doke ‘yar wasa Iga Swiatek ‘yar kasar Poland da ci 6-4 da 6-1.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!