Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Messi ka iya komawa Barcelona – Carrasco

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta
Barcelona Lobo Carrasco ya ce dan wasan gaba na PSG Leo Messi ka iya komawa filin wasa na Nou Camp a kakar wasanni da muke ciki.

Dan wasa Carrasco ya kuma ce idan har kungiyar da Messi ke fafatawa wasa ta gaza lashe gasar cin kofin zakarun turai Champions League shakka babu ya na da kwarin giwa Leo zai komawa Barcelona.

Tsohon zakaran dan wasan ya bayyana hakane yayin da yake zantawa da gidan talabijin na El Chiringuito TV a makon da muke ciki.

“Na lura da yadda dan wasan ke da mahimmanci, wanda nake fata da kuma tabbacin Messi ka iya komawa tsowur da ya fafata wasa a baya, duba da yadda gasar cin kifin zakarun turai Champions League ke daukar sabon salo,”

“Yanayin da ya ke ciki matuka na da tsauri, amma komawarsa zuwa Barcelona shi ne zai fi zama abu mafi sauki gareshi,” a cewar Lobo Carrasco.

Lobo Carrasco ya kara da cewa “Messi baya jin da din zaman da ya ke a birnin Pari na kasar Faransa, sakamakon haka ya sa yadda ya ke taka leda ba kamar yadda ya ke a Barcelona.

Leo Messi dai a gasar Ligue 1 kwallo daya kawai ya zura a wasanni 12 da ya buga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!