Labarai
Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, yana mai bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an ‘yansanda da na soja.
Shugaban wanda ya bayar da umarnin yayin wani jawabi a fadarsa, ya bai wa rundunar ‘yansandan ƙasar umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai 20,000.
Ya ce adadin sababbin jami’an da za a ɗauka yanzu ya zama 50,000, bayan umarnin da ya bayar ranar Lahadi na ɗaukar 30,000.
Ɗaya daga cikin mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya faɗa wa BBC cewa dokar na nufin ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro a faɗin Najeriya.
Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka ta Forest Guard.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ‘yanta’adda da ‘yanfashi daga dazuka”.
“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
You must be logged in to post a comment Login