Connect with us

Labarai

Tinubu ya bukaci yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya da nufin bai wa jihohi damar kafa ‘yan sanda duba da yadda matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara  a fadin ƙasa. 

 

Tinubu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da majalisar wakilai ta shirya a Abuja, da aka tattauna kan tsarin tsaron kasa da kuma bukatar sabunta kundin tsarin mulki. 

 

Shugaban wanda Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya wakilta, ya bayyana cewa tsaron kasa na bukatar sababbin hanyoyin warwarewa duba da sauye-sauyen zamani.

 

Tinubu ya bukaci a sauya tsarin da ke sanya ‘yan sanda a karkashin dokar majalisa ta tarayya kawai, domin ba wa jihohi damar kafa nasu rundunar ‘yan sanda, matakin da zai inganta tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!