Labarai
Tinubu ya tafi zuwa Turai domin kammala hutun shekara

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bar Legas a yau Lahadi zuwa Turai don cigaba da hutunsa na karshen shekara.
ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa shugaban zai kuma kai ziyara a hukumance zuwa Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Shugaban ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne ya gayyaci Tinubu domin halartar wani taro na mako ɗaya kan ɗorewar cigaba na 2026, wanda za a gudanar a farkon Janairun sabuwar shekara.
Kakakin na Tinubu ya ce taron na tsawon mako ɗaya an saba yin sa ne domin haɗa shugabannin gwamnati, ƴan kasuwa da kuma al’umma don tattaunawa a taron.
You must be logged in to post a comment Login